Jambtu ta samu sabon shugaban PCRC

An kirayi masu ruwa da tsaki dake cikin unguwar Jambutu a karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa da sukasance masu hada kansu da Kuma yin aiki tare domin Samar da zaman lafiya dama cigaban unguwar harma da jaha baki Daya. Sabon shugaban kwamtin dake taimawa rundunan yan sanda a unguwar Jambutu wato PCRC Alhaji Adamu Jingi ne ya yi wannan kira Jin kadan da nadishi shugaban kwamitin na Unguwar Jambutu. Alhaji Adamu Jingi ya Kuma kirayi masu ruwa da tsakin da su kasance ana samun kyakkawar halaka a tsakanin su tare Kuma da taimakawa hukumomin tsaro domin Samar da zaman lafiya a Unguwar dama jaha baki Daya. Adamu ya Kuma shawarci Yan siyasa da su maida hankali wajen koyawa matasa sana o i domin ganin sun dogara da kansu. Ya Kuma kirayi matasa da sukasance sun maida hankali wajen Neman sana o I dogaro da Kai Wanda hakan zai taimaka wajen kare mutuncinsu a indon Al umma. Alhaji Jingi ya Kuma godewa Allah ma daukin sarki bisa bashi wannan matsayin tare da godewa tawagam da sukazo suka tabbatar masu da wannan shugabanci. Don haka yace zaiyi dukkanin Mai yiwa domin tabbatar da hadin Kai dama cigaban Unguwar ta Jambutu. Shima anashi bangaren mataimakin sakataren kwamitin na PCRC na shiyar a Prince Sa ad Ibrahim Gurin kira yayiwa kwamitin da akoda yaushe sukasance masuyin aiki tukuru dama yin aiki tare domin ganin an samu nasara. Sa ad Ibrahim Gurin ya Kuma shawarci Al umma da sukasance suna baiwa kwamitin hadin Kai da goyon baya domin ganin an samu nasaran dakile matsalar tsaro a fadin jahar baki Daya. A jawabainsu daban daban Mr Isma ila Maikyau shugaban CTC PCRC A jahar Adamawa, Sa ad Maigari mataimakin sakataren CTC PCRC a jahar Adamawa, da Habiba Abdullahi ko odinata Kuma taskar CTC PCRC na jahar Adamawa dukkaninsu sunyi kirayi membobin kwamitin da akoda yaushe sukasance masu hada kansu domin Samar da zaman lafiya dama cigaban Al umma.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE