Kamfainin Dangote ya Sha alwashin inganta rayuwar Al ummomin dake kewaye dashi.

kamfanin Dangote dake karamar hukumar Numan a jajar Adamawa ya kara jaddada aniyar sa na inganta rayuwar al'ummomin dake kewaye da it. Shugaban sashin aiyuka na kamfanin, Alhaji Bello Dan Musa ne ya baiyana haka yayin taron masu ruwa da tsaki da kamfanin ya shirya a karamar hukumar Numan na jahar Adamawa. Shugaban sashin aiyukan, Bello Dan Musa yace makasudin shirya wannan taron masu ruwa da tsakin dai shine domin karfafa mu'amala tsakanin yankunan, da yi musu karin bayani kan aiyukan Kamfanin Dangote da kuma sauraron koke koke da suke da su idan akwai, kana a hadu a nemo mafita tare. Dan Musa yace i zuwa yanzu, duk alkawarin da kamfanin ta dauka ta cika, kama daga horas da matasa zuwa daukan nauyin karatun dalibai da tayi, ganin yanzu wadanda aka baiwa horon sun kammala, kana dalibai na cigaba da karatu karkashin tsarin daukan nauyin su, tare da karin cewa kamfanin na shirin diban wasu karin dalibai 160 domin cin gajiyar shirin daukar nauyin karatun. Bello Dan Musa yace har wa yau, karkashin shirin ta na noma wato out growers scheme, kamfanin da biya manoma kudade da suka haura Naira miliyan dari biyar, kuma tana nan tana taimakawa jami'an tsaro gurin kare rayuka da dukiyoyin matafiya da ke bin wadannan yankuna. Yayin da yake isar da sakon gaisuwan shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, shugaban sashin aiyukan ya godewa wadannan al'ummomi da irin hadin kai da suke baiwa kamfanin tare da kira gare su da su ci gaba da hakuri da juna domin cin moriyar mu'amalataiya dake tsakanin su. Yayin da suka yi nasu jawabin, hakimin Garin Lafiya , Clement Minakaro, da hakimin Mbula, Afraimu Fwa, da kuma hakimin Borrong, Chief Lawson Gadiel Nayina dukkanin su sun godewa kamfanin Dangote da shirya wannan taro, wanda suka ce zai yi tasiri matuka gurin karfafa dangantaka tsakanin al'ummomin yankin da ma kamfanin baki daya. Yayin da suke kira ga matasa da suyi amfani da wannan dama basu horo da ɗaukan nauyin karatun su, shuwagabannin gargajiyan sun ja hankalin al'ummomin yankin da su zauna lafiya tare da juna, sukuma ci gaba da baiwa kamfanin Dangote hadin kai da goyon baya da ya kamata. Cikin wadanda suka halarci zaman dai sun haɗa da hakimai, masu anguwanni, shugabannin matasa da jagororin mata wadanda suka fito daga kananan hukumomin Numan, Lamurde, Demsa, Guyuk da kuma Shelleng.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.