Kungiyar malamain Jami o I a Najeriya ASUU ya yabawa gwamnatin tarayya kan cire Jami o I daga tsarin biyan Albashi na IPPIS.
malamain Jami o I a Najeriya wato ASUU ta yabawa gwamnatin maici karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu bisa kokarinta na cire Jami o in Najeriya dama sauran manyan makarantu daga tsarin biyan albashi na IPPIS a wani mataki na inganta manyan makarantu dake fadin Najeriya
Shugaban Kungiyar ta ASUU shiyar Jami ar Modibbo Adama dake Yola Dr El Maude Jibrin ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
A cewarsa cire Jami o in Najeriya dama wasu manyan makarantu daga tsarin na IPPIS da akayi a kwanan nan Yana Daya daga cikin matakai da wannan gwamnati karkashin shugaban Bola Ahmed Tinubu na inganta tsarin Jami o I dake fadin Najeriya.
Dr El Maude yace gwamnatin da ta gabata karkashin tsohon shugaba Muhammadu Buhari ala tilas ta sanya Jami o I dama manyan makarantu cikin tsarin na IPPIS .
Dr El Maude Jibrin ya Kuma yaba da kokarin da ministan ilimi Farfesa Tahir Mamman yakeyi na tabbatar da ganin an cire Jami o I dama sauran manyan makarantu daga tsarin na biyan albashi na IPPIS.
Ya Kuma bukaci ministan da ya maida hankalin kan yarjejeniua da kungiyar ta ASUU ta cimma da gwamnati tun a shekara ta 2016 Wanda ya hada da alawus alawus nasu da dai sauransu.
Ya Kara kira ga gwamnati da tayi dukkanin maiyiwa domin inganta yanayin aiyukan Jami o I domin cigaban kasa baki Daya.
Comments
Post a Comment