Kungiyar NASWDEN Shiyar karamar hukumar yola ta Arewa ta rantsar da sabbin shuwagabanninta a jahar Adamawa.

An kirayi shuwagabanin masu sana ar kayakin Bola a jahar Adamawa da su kasance masu gudanar da shugabancin su bilhakki da gaskiya domin ganin an samu cigaban kungiyar yadda ya kamata a fadin jahar ta Adamawa. Shugaban dattawan kungiyar masu sana ar kayakin Bola a jahar Adamawa Alhaji Aiwalu Bashiru ne yayi wannan kira a lokacinda yake jawabi a wurin bikin rantsar da shuwagabanin kungiyar na shiryar karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa. Alhaji Auwal Bashiru yaja hankalin shuwagabanin da su maida hankali wajen kare martabar kungiyar a idon Al umma da Kuma gudanar da aiyukan cigaban kungiyar dama tsafcaceta domin ganin an daina kallon kungiyar da mamunan zato. Haka kazalika ya kirayi kwamitin cika aikin kungiyar da su Kara hazaka domin zakulo dukkanin masu yiwa kungiyar zagon kasa ko natawa kungiyar suna domin Yi musu hukunci. Domin acewarsa akwai wasu dake gudanar da aiyukansu ba bisa Ka idaba da sunan kungiyar. Shima a jawabinsa kwamandan rundunan tsaro bada kariya ga fararen hula wato Civil defence a jahar Adamawa Ibrahim Mai Nasara Wanda mataikain kwamandan DCC Alkali ya wakilta kirayi wa shuwagabanin kungiyar da sukasance suna baiwa rundunan hadin da goyon baya a Koda yaushe domin ganin an samu nasaran kakkabe bata gari a cikin kungiyar. Ya Kuma taya sabbin shuwagabanin murna tare da shawartansu da su maida hankali wajen hadin kan kungiyar dama cigaban kungiyar. Ya Kuma tabbatarwa shuwagabanin kungiyar cewa rundunan a shirye take ta baiwa kungiyar hadin Kai da goyon baya domin ganin ta gudanar da aiyukan ta yadda ya kamata ba tare da matsalaba.
Da yake nashi bawabi sabon shugaban kungiyar masu sana ar kayakin Bola na karamar hukumar yola ta arewa Alhaji Muhammed Sabi u Rabi u ya godewa Allah ma daukakin sarki dangane da wannan dama da ya bashi. Ya Kuma baiyana farin cikinsu tare da godewa membobin kungiyar bisa zabarsa a matsayin shugaban kungiyar a karamar hukumar yola ta arewa. Alhaji Sabi u ya Kuma tabbatar da cewa zai gudanar da aiyukansu kafada da kafada da shuwagabanin kungiyar Damon ciyar da kungiyar gaba. Don hakanema yake kira ga membobin kungiyar da sukasance suna baiwa shuwagabanin kungiyar hadin Kai da goyon baya domin ganin sun cimma burinsa na kare martabar kungiyar. Taron dai ya samu halartan membobi dama shuwagabanin kungiyar daga sassa daban daban na ciki da wajen jahar Adamawa.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE