Kungiyar yan Jarida a jahar Adamawa ta taya Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri murnan samun nasara a kotun daukaka Kara.

Kungiyar Yan Jarida a Najeriya NUJ shiyar jahar Adamawa ta taya Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri murnan nasara Da ya samu a kotun daukaka Kara a zamanta da tayi a Abuja. Kotun ta sake tabbatarwa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri cewa shine yayi nasaran zaben gwamna a jahar Adamawa. Kungiyar ta NUJ ta baiyana hakane a wata sanarwa da ta fitar dauke da sanya hanun shugaban kungiyar a jahar Adamawa Ishaya Donald Dedan tare da sakatarenta Fedelis Jockthan Wanda suka fitar a yola. A cewar Kungiyar nasaran da gwamnan yayi ya nuna cewa Allah ma daukakin sarki ya baiwa mutane jahar Adamawa abunda suka zaba Wanda Kuma hakan zai baiwa gwamnan daman gudanar da aiyukan cigaban jahar ta Adamawa. Saboda haka kungiyar ta kirayi Al ummar jaha dama Yan adawa da suzo a hada Kai domin baiwa gwamnatin Ahmadu Umaru Finti baya domin samun cigaba harma da zaman lafiya. Kungiyar tace tana fatan dukkanin Yan adawa zasuyi aiki kafada da kafada da gwamna fintiri domin ciyar da jahar gaba.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE