Majalisar Addinin Musulunci a jahar Adamawa ta jajantawa iyalen wadanda suka rasa yan uwansu a harin bom a jahar Kaduna.

Majalisar Addinin musulunci jahar Adamawa tayi baiyana takaicinta da alhininta dangane da harin bom da aka Kai akan masu gudanar da bikin maulidi a kyauwain Tudun biri dake cikin karamar hukumar Igabi a jajar Kaduna. Babban sakataren majalisar a jahar Adamawa Mallam Ismaila Modibbo Umar ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola. Mallam Isma ila yace harin baiyi daidaina Kuma wannan abune da baikamataba, saboda haka malalisar tana kira ga gwamnatin tarayya dama masu ruwa da tsaki da suyi dukkanin abinda suka dace domin gudanar da bincike kan lamarin domin daukan mataki da ya dace kan wadanda suka aikata wannan aiki na hallaka ratuwakan mutane da dama harma da jikkata wasu. Ya kara da cewa irin wannan lamari yasha faruwa na tare da an dauki mataki a kaiba don haka ya zama wajibi gwamnatin tarayya dama gwamnatin jahar Kaduna su gudanar da bincike kwakwaf domin hukunta duk wadanda suke da hanu a cikin lamarin. Mallam Ismaila ya Kuma baiyana ta aziyar majalisar Addinin musulunci dake jahar Adamawa ga iyalen wadanda suka rasa yan uwansu tare da yi musu adu ar Allah ya gafarta musu yasa Aljannace makomarsu. Ya Kuma yi Adu ar Allah madaukakin sarki ya baiwa wadanda suka jikkata sauki Allah ya Kare tare da yi musu fatan samun sauki cikin gaggawa. Harwayau majalisar taji ya baiyana farin cikinta dangane da yadda Al umma musulamai dama wadanda ba musulmaiba ke ta nuna alhinunsu dangane da lamarin. Don haka ya kamata kungiyoyi dama masu ruwa da tsaki su tabbatar anyiwa wadanda lamarin ya shafa adalci. Majalisar ta Kuma kirayi Al umma musulamai sukasance masu hada kansu a Koda yaushe domin samun cigaba addinin musulunci a tsakanin Al umma, baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE