Mata 100 ne dai aka koyawa sana oi daban daban a jahar Adamawa.

Daga Ibrahim Abubakar yola.
A kalla mata dari biyar ne aka koyawa sana o I daban daban domin dogara da kansu a jahar Adamawa. Shugaban sashin shirye shirye na yankin Arewacin Najeriya a ma aikatar harkokin Jinkai da rage radadin talauci ta tarayya Farida Musa Jauro ce ta dauki dawainiyar koyawa mata sana o in a jahar Adamawa. Matan dai sun samu horon ne akan sana o I daban daban da suka hada da koyon yin jaka, mangashi,da dai sauransu Kuma an zakulo matanne daga yankin Mubi dake jahar Adamawa. Farida Musa tace an koyar da mata sana o in ne da zumar ganin sun samu sana ar dogaro da Kai ganin yadda suke fama da dawainiyar gida. A cewarta wannan taimako yana daga cikin aniyar gwamnatin tarayya samarwa yan Najeriya aiki domin bunkasa tattalin Arzikin kasa baki Daya. Ta Kuma Kara da cewa an gudanar da irin wannan koyar da sana o I a wasu sassan kasan nan domin rage radadin talauci a tsakanin matan Najeriya. Farida ta yabawa monistar ma aikatar Jinkai da rage radadin talauci Dr Betta Edu bisa goyon bayanta dangane da koyar da sana o I da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya amincce da Shirin domin inganta rayuwar mata. Ta Kuma jaddada aniyar gwamnatin karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu na rage radadin talauci dama Samar da aikinyi tare da Kiran wadanda suka amfana da Shirin da suyi amfani da abinda suka koya domin samun cigaban Al umma. Da yake magana a wurin taron Hakimin Yadafa dake cikin karamar hukumar Mubi ta kudu Mallam Baba Galaduma ya yabawa Hajiya Farida bisa kokarinta na kawo wannan ahiri a yankin na Mubi tare da Kiran wadanda suka samu horon da suyi amfani da abinda suka koya ta hanyar da ta dace domin inganta rayuwar su yadda ya kamata. Ya Kuma mika gidiyarsa na musamman ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa kokarinsa na Samar da tsare tsaren da zasu inganta rayuwar jama a ya Kuma yabawa ministar ma aikatar Jinkai da rage talauci bisa goyon bayanta dangane da Shirin. A jawabinsu Dan majalisar Mai wakilta Mubi ta arewa a majalisar dokokin jahar Adamawa Yohana Musa Jauro da tsohon Dan majalisar maiwakilyan Kada Mbulo Hammanjpda Umar Farang dukkaninsu sun yaba da wannan Shirin na Farida da ta taimakawa mata Suma sun kirayi matan da sukaci gajiyar Shirin dasuyi amfani da ilimin da suka samu yadda ya dace. Wasu daga cikin wadanda suka amfana da Shirin irinsu Rabeca Maina, Maryam Ahmed, Hauwa Buba, sun baiyana godiyarsu ga Hajiya Farida da shigaba Bola Tinubu dama ministar Dr Betta Edu bisa koya musu sana o I da zasu dogara da kansu. Sun Kuma Yi alkawarin yin amfani da abinda suka koya domin inganta kasuwancinsu da ma rayuwarsu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE