Rundunan soji Dana Yan sanda sun lashi takwabin inganta tsaro a fadin jahar Adamawa.
Yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya karbi bakoncin sabon kwamandan Bataliyar sojoji ta 23 dake Yola Brigadire General P K Zawaye a ofishinsa inda suka tattauna batun hadin Kai da Kuma samun saukin inganta tsaro a fadin jahar.
Hakan na kunshene acikin wata sanarwa daga kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje Wanda ya rabawa manema labarai a Yola.
Kwamnadan ya kawo ziyaranne tare da manyan Jami an rundunan sojojin na Bataliya ta 23 domin su tattauna hanyouin da za abi domin ganin an samu kyakkawar hadin Kai a tsakanin rindunonin biyu domin magance dukkanin kalubalen tsaro dake ciwa Al umma tuwo a kwarya.
Kwamandan ya Kuma tabbatar wa kwamishinan cewa zaiyi dukkanin abinda suka dace domin ganin an samu hadin Kai da kyakkawar halaka a tsakanin Jami an rindunonin biyu saboda ganin anbi doka da oda. Ya Kuma yabawa kwamishinan bisa na mijin kokari da yake Yi wajen ganin anbi doka da oda tare da masa alkawarin cewa zai bada hadin Kai da goyon baya domin ganin Jami an masu sun samu horo domin ganin an samu damar kare rayuka dama dukiyoyin Al umma.
Shima a jawabinsa kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya baiyana cewa ziyaran da kwamandan ya kawo ya nuna cewa akwai kyakkawar halaka a tsakanin rindunonin biyu saboda haka akwai bukatar hadin Kai Wanda hakan zai taimaka wajen inganta tsaro a fadin jaha. A cewarsa Yana da muhimmanci a samu fahintar juna da Kuma yin aiki kafada da kafada tare da Kiran Jami an da sukasance masu hada kansu a Koda yaushe domin samun cigaba dama zaman lafiya Mai daurewa.
Comments
Post a Comment