Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta kirayi Al umma da sukasance masu baiwa hukumomin tsaro hadinkai.

A yayinda kwanaki kadan ya rage a gudanar da shagulgulan bikin shigowar sabuwar shekara Wanda za ayi ran 31-12-2023 Wanda Kuma a lokacin Sa o I kadan suka rage a shiga sabuwar shekara wato ran litini 1-1-2-24. Hakan yasa rundunan yan sandan jahar Adamawa tana Mai sanar da cewa za a takaita zirga zirgan ababen hawa a hanyan Saman shataletalen Yan sanda take Yola. Saboda haka wadanda suka fito daga filin jirgin Sama zasuyi Yola to daga shataletalen fire service sai su nausa bekaji su bulla zuwa sakatariyar tarayya, sai Kuma Wanda suka fito daga Yola zasuyi Titin Numan sai subi Dougire zuwa dandalin Mahmud Ribadau zuwa Mahadar taget sai su bulla ta shatale talen fire service. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema labarai a Yola. Sanarwa tace za a gudanar da shagulgulane a shataletalen hanyar Saman Yan sanda wato kusa da shelkwatan Yan sanda jahar ta Adamawa. Sanarwan ta Kara da cewa an dauki dukkanin matakan tsaro a wurin da za a gudanar da shagulgulan bikin domin kuwa rundunan da takwaririnta na tsaro sun hada gwiwa domin ganin an samu wadaceccen tsaro. Rundunan ta Kuma shawarci masu ababen hawa da su ajiye ababen hawansu daga nesa daga inda za ayi bikin Kuma kar mutane su razana domin za jibge Jami an tsaro a wurare daban daban harma da kafa shingen bincike da dai sauransu. Harwa yau rundunan ta kirayi Al umma da su bada hadinkai da goyon baya wa hukumomin tsaro domin ganin an kammala bikin lafiya na tare da matsaloliba.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE