Rundunan yan sandan jahar Adamawa tana tsare da wani da ake zargi da kashe akawun kotu.

Rundunan yan sandan jahar Adamawa yanzu haka tana tsare da wani Mai Suna Linus Dimas Dan shekaru 43 mazanin Kugama wuri Jibir dake cikin karamar hukumar Mayo Belwa daka jahar Adamawa. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da rabawa manema labarai a Yola. Wanda ake zargin dai an kamashine sakomokon kashe akawun kotu biyo bayan dabasa wuka a lokacin da ya Kai masa takartan dammace daga wata kotu daka Nasarawa Jereng inda ya cacakawa akawaun kotun Mai Suna Ya uba Usman wuka lamarinda yasa ya samu rauni sosai Wanda Kuma hakan yasa aka garzaya da shi zuwa asibitin daga bisani aka tabbatar ya mutu. Kawo yanzu dai kwamishinan Yan sanda jahar Adamawa Afolabi Babatola ya bada umurnin gudanar da bincike kan lamarin.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE