Shugaban kwalejin ahar wato SPY yaiwa gwamna gaisuwar bikin kirsimeti.
ban kwalejin fasahar ta jahar Adamawa wato SPY Farfesa Muhammed Dahiru Toungos a madadinsa dama ma aikatan kwalejin na masu farin cikin taya Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da mataimakiyatsa Farfesa Kaletapwa George Farauta da kakakin majalisar dokokin jahar Adamawa Hon. Bathiya Wesley, membobin majalisar zantawar jahar Adamawa dama na majalisar dokokin jahar murnan bikik kirsimeti na wannan shekara ta 2023.
Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Farfesa Muhammed Dahiru Toungos har wayau ya taya Al ummar jahar Adamawa inda yace ana gudanar da bikin na kirsimeti ne domin tunawa da ranan haifuwar Annabi Isa AS da Kuma yin koyi da jalayensa.
Shugaban kwalejin ta SPY ya shawarci mazauna jahar ta Adamawa da kada suyi amfani da wannan lokaci ta yin abida bai dace ba. Kamatayayi suyi amfani da wannan lokaci waken yin adu o I domin Neman hadin Kai dama zaman lafiya harma da cigaban jahar ta Adamawa baki Daya.
Da wannan yake kira ga Al ummar jahar Adamawa da sukasance suna baiwa gwamna Ahmadu Umaru Finti hadin Kai da goyon baya domin ya samu damar gudanar da aiyukan cin moriyar domokiradiya a fadin jaha.
Ya Kuma yi fatan Allah ya karawa gwamna lafiya ya Kuma bashi nasaran cigaba da aiyukan da yakeyi ya Kuma Yi biki wannan shekara lafiya.
Comments
Post a Comment