An nada sabon wakilin waja a karamar hukumar Guyuk.
Sarkin Guyuk Kwandi Nunguraya Dr Kurhaye Diahon Dansanda II ma nada Alhaji Muhammadu Gajere Ajiya a matsayin Wakilin waja.
Alhaji Muhammadu Gajere Ajiya Wanda Kuma shine sabon wakilin waja Dan uwane ga tsohon Babban sakataren a ma aikatar harkokin kananan hukumomi da sarakunan Mr Japhet Gajere.
An Yi bikin nadin wakin wajan ne a fadar sarikin Guyuk dake cikin karamar hukumar Guyuk dake jahar Adamawa.
.
An dai baiyana wakilin waja a matsayin mutuminda ya cancanta Kuma Wanda ya bada mhimmiyar gudamawa wajen Samar da zaman lafiya a tsakanin kabilin Lunguda da Kuma Waja. Wanda hakan ya aka ga ya dace a bashi wannan saraitar ta wakilin waja.
.
Da yake jawabi a lokacin nada wakilin na waja a kashen mako Kwandi Nunguraya ya tayashi murna tare da kiranshi da ya gudanar da aiyukansa yadda ya kamata domin samun cigaban zaman lafiya a tsakanin Al ummar yankin.
..
..
Basaraken yayi amfani da wannan damar domin kabilun wato Lunguda da Waja da sukasance masu hada kansu Kuma su zauna da juna lafiya domin ganin an samu nasaran Kai yankin ga samun cigaba domin a cewarsa ana samun cigabane da zaman lafiya.
Ya Kuma tunatar da sabon wakilin na Waja da yayi dukkanin abinda suka dace domin samun cigaban masarautar dama Al ummar yankin baki Daya.
Anashi bangaren Hakimin Ginakise Wanda Alhaji Muhammed Danjumma Muhammed ya wakilta yana Mai godewa Allah madaukakin sarki da aka samu zaman lafiya a tsakanin Lunguda da Waja.
Alhaji Danjuma ya Kuma shawarci matasa da su nisanta kansu daga duk abinda zai kawo rarrabuwan Kai a tsakanin Al umma Mai makon haka suyi abunda zai kawo zaman lafiya da hadin Kai harma da cigaban yankin.
.
A nashi jawabi sabon Wakilin na Waja Alhaji Muhammadu Gajere Ajiya ya godewa masaraken wato Dr Kurhaye Dishon Dansanda II dama majalisar masarautar Lunguda da ya nadashi a matsayin Wakilin Waja. Wanda wannan wata damace da zata Kara masa kwarin gwiwa cigaba dayin dukkanin abinda zai kawo cigaban masarautar ta Lunguda.
Alhaji Gajere ya tabbatar da cewa zai dukkanin maiyiwa domin Samar da cigaban masarautar ya Kuma kira da abashi hadin Kai da goyon baya domin ganin ya samu nasaran gudanar da ahugabancinsa yadda ya kanata.
Ya Kuma baiyana gamsuwarsa dangane da yadda aka gudanar da bikin tare dayin A du a domin Neman taimakon Allah Madaukakin sarki ya bashi nasaran kan aniyarsa na wanzar da zaman lafiya a tsakanin Al ummar yankin baki Daya.
Comments
Post a Comment