Gwamna Inuwa Yahaya na jahar Gombe ya bukaci hadinkai a tsakanin gwamnoni Arewa.

Shugaban Kungiyar gwamnoni yankin Arewacin Najeriya Kuma gwamnan jahar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya yace dolenefa shuwagabanin arewa sukasance suna magana da murya Daya in har ana so a magance dukkanin matsàloli da yankin ke fuskantar domin Samar da zaman lafiya. Kamar yadda marigayi sir Ahmadu Bello yayi. Shugaban Kungiyar ya baiyana hakane a wajen taron lacca na tunawa da Ahmadu Bello Wanda akeyi shekara shekara Wanda ya gudana a Maiduguri fadar gwamnatin jahar Borno. Gwamnan ya baiyana cewa akwai bukatar yin koyi da halayen Sardauna domin ganin an samu dai dai to a tsakanin shuwagabanin da Al umma Wanda hakan zai taimaka wajen warware dukkanin kalubalen da yankin Arewacin Najeriya. Ya Kuma shawarci takwaririnsa da suk asance masu Samar da dabaru da zasu taimaka wajen magance matsalar tsaro a yankin baki Daya Gwamna ya Kuma baiyana cewa yana da muhimmanci an wadatar da Al umma da kayakin more rayuwa illimi, kiwon lafiya, da basu damar bunkasa tattalin Arziki da Kuma yin adalci da gaskiya. Da yake magana dangane da gudumawa da Ahmadu Bello ya bayar a lokacin rayuwarsa Gwamna Inuwa Yahaya yace Ahmadu Bello ya taka rawan gani wajen cigaban kasa saboda haka akwai bukatar daukan salon kamar na marigayi domin Samar da hadin Kai dama zaman lafiya Shima anashi jawabi tsohon gwamna jahar Neja ya yaba da irin shugabancin gwamna Inuwa Yahaya yakeyi a jahar Gombe dama shugabancin kungiyar gwamnoni na yankin Arewacin Najeriya. .mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima Wanda mataimaki na musamman ga shugaban kasa Dr Hakeem Baba Ahmed ya wakilta Shima ya bada shawaran hadin Kai domin cigaban Najeriya Bako Mai jawabi Kuma wakilin Najeriya a majalisar Dinkin duniya Farfesa Tijjani Bande yace akwai bukatar Samar da tsarin da ya dace domin magance dama kawar da kalubalen da ake fuskanta a wani matakai na cigaban kasa baki Daya Sauran masu gabatar da jawabai ciki harada Mai masaukin baki Farfesa Babagana Umara Zulum yace taron ya gudana a lokacin da yakanata Kuma akan lokaci da zai taimaka wajen cigaban Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.