Hukumomin tsaro a Najeriya sunsha aradun kawo karshen hakan ma adinai ba bisa kaidaba a fadin Najeriya.
A kokarin ta na inganta tsaro gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu ta kudiri aniyar inganta hakan muadinai a Najeriya Wanda hakan yasa gwamnatin ta Samar da wani kwamitin hadin gwiwar hukumomin tsaro a wani mataki na dakile matsalar hakan mu adinai ba bisa kaidaba a fadin Najeriya.
Kawo yanzu dai kwamitin ya gudanar da zamansa a shelkwatar rundunan yan sandan Najeriya, Wanda ya samu wakilain hukumomin tsaro da suka hada da sojoji, civil defence, ma aikatun mu adinai dama sauran hukumomin da lamarin ya shafa .
Kakakin rundunan yan sanda ta kasa dake ahekkwatar ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Sanarwan ta baiyana cewa aiyukan kwamitin dai shine yin dukkanin maiyiwa domin dakile hakan ma adinai ba bisa Ka idaba walau Yan kasashen wajene ko Kuma Yan Najeriya ne.
Kwamitin zai Kuma inganta tsaro a dukkanin inda ake hakan Muadinain da Kuma tabbatar da ganin anbi doka domin samun cigaban aiyukan hakan mu adinai.
Rundunan yan sanda dama sauran hukumomin tsaro suna nan domin bada goyon baya ga aniyar gwamnatin tarayya na bunkasa tattalin Arzikin kasa domin samun cigaban Najeriya.
Comments
Post a Comment