Iyaye sun yabawa gwamna Kefas na Jahar Taraba.

Daga Sani Yarima Jalingo
Mazauna jahar Taraba musammanma iyaye sun yabawa gwamna Agbu Kefas na jahar Taraba bisa kokarinsa na baiwa daluben jahar illimi kyauta. Iyaye sun bauyyana yabon ne a zantawarsu da wakilinmu Jalingo fadar gwamnatin jahar Taraba.
Iyayen da suka hada da Malam Kasimu Garba, Agnes Andrew, Isa Jauro, da Innocent Apollo's dama wasu iyayen duk su baiyyana cewa wannan tsarin na bada illimi kyauta tsarine da zai baiwa yara damar samun ingancaccen illimi ba tare da matsalar kudiba Kuma hakan shinema moriya domokiradiya. Sukace duba ta matsin tattalin Arziki dake addabar gwamnatin a yanzu dama Yan Najeriya Wanda hakan yasa iyaye da dama bazaai iya daukan dawainiyar yaransuba saboda rashin kudi.
Iyayen sukace tsarin na bada Illimi kyauta hakan zaitaimaka wajen rage yawan yaran da suke gararanba a kan titi basazuwa makaranta saboda iyaye zasu samu damar tura yaransu makaranta biyo bayan wannan cigaba da aka samu don suna mika godiyarsu ga gwamna bisa wannan taimako. Sun Kara da cewa yabon ya zama wajibi duba da yadda ya maida hankali wajen bada illimi kyauta Wanda Kuma irinsa na farko a tarihi a jahar. Iyayen sun Kuma kirayi daukacin Al ummar jahar da su cigaba da yin adu o I domin gwamna Kefas ya samu nasaran gudanar da aiyukan cigaban jahar.
Harwayau Malam Kasimu Garba, Agnes Andrew, da Innocent Apollo's sun yabawa mukaddaahin shugaban hukumar bada illimi bai Daya ta jahar Taraba Mis Rabi Sunday bisa kokarinta na aiwatar da aniyar na gwamna Agbu Kefas na inganta sashin illimin jahar. Inda suka baiyanata a matsayin mace Mai kamanmaza wajen jajircewa domin bunkasa harkokin illimi da Kuma cigaban hukumar. A cewar iyayen a kwanan nan sun shaida yadda aka rarraba kayakin karatu a makarantu daban daban dake cikin kananan hukumomin Sha shida dake fadin jahar. In za a iya tunawa dai a makon da ta gabata hukumar ta TSUB ta rarraba wasu kayakin karatu da suka Kai na milyoyin nerori a makarantu daban daban dake fadin jahar. Wakilin namu Wanda Yana cikin tawagan da suka Kai ziyaran a makaratun tsangaya ya rawaito mana cewa tawagan sun yaba da yadda lamura ke tafiya a makarantu da Kuma yin amfani da kayakin da aka basu ta hanyar da ta dace. A karshe dai sun taya Gwamnan murnan samun nasara da yayi a kotun koli.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE