Kungiyar Yan Jarida a jahar Adamawa ta taya Gwamna Fintiri murnan nasara da yayi a kotun koli.

Kungiyar yan Jarida a Najeriya NUJ shiyar jahar Adamawa ta taya Gwamnan jahar Adamawa murnan samun nasara da yayi a kotun koli Najeriya.
Kungiyar ta baiyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar Yola dauke da sanya hanun shugaban kungiyar a jahar Adamawa Isyaka Donald Dedan tare da sakatarenta Fidelis Jockthan.
.A sanarwan an baiyana cewa hukunci na kotun koli ya tabbatar da cewa Allah ya baiwa Al ummar Wanda suka zaba .Wanda Kuma ya tabbata cewa Yan Najeriya zasuyi Amanna da bangaren shariya Najeriya.
Kungiyar ta NUJ tace wannan hukunci wani matakine na tabbatar da daurewar domokiradiya da Kuma cigaban harma da zaman lafiya.
Har wayau kungiyar ta kirayi Yan adawa da Al ummar jahar Adamawa da su baiwa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri goyon baya domin ganin ya kammala wa adin mulkinsa lafiya ba tare da matsalaba.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE