An kirayi gwamnatin tarayya da kada tayi da wasa wajen daukan matakin dakile tsadar rayuwa da ake ciki a halin yanzu.

 



An kirayi gwamnatin tarayya da ta dauki dukkanin matakai da suka dace domin kawo karshen halin ha ula I da ake cikin a halin yanzu a fadin kasan nan domin Samar da zaman lafiya mai daurewa a fadin Najeriya.



Babban sakataren kungiyar Jama atu Nasaril Islam ta kasa Farfesa Khalid Abubakar Aliyu ne yayi wannan kira a lokacinda yake jawabi a wurin bude taron kungiyar ta  kasa da akayi a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.




Farfesa Khalid yace ya zama wajibi sukirayi gwamnatin tarayya dangen da halin da Al umma suka tsinci kansu na tsadar rayuwa, saboda haka ya wajaba ga gwamnatin tarayya da tayi dukkanin Mai yiwa domin zakulo hanyoyin da suka dace domin ganin Al umma sun fita daga wannan hali da suke ciki.



Ya Kuma masu hanu da shuni da suyi amfani da wannan lokaci musammanma da aka fuskanci watan Ramadan da Suma sukasance suna taimakawa marassa galihu domin Suma su samu saukin raguwa a tsakanin Jama a.




Farfesa Khalid ya Kuma ja hankalin malamai musammanma masu gabatar da wa azizzuka a watan Ramadan da sukasance masuyin taka tsantsan domin kaucewa kalamain batanci ga kungiyoyi ko wani maimakon haka su maida hankali wajen dukkanin abinda zai kawo zaman lafiya dama cigaban kasa baki Daya.



Tunda farko a jawabinsa na maraba shugaban kungiyar Jama Atul Nasaril Islam. Jahar Adamawa  Alhaji Mustafa Aminu galadiman Adamawa ya godewa Allah madaukakin sarki da ya basu damar gudanar da wannan taro tare da marabtan mahalartam taron da sukazo daga sassa daban daban a fadin Najeriya. Inda yayi Adu ar Allah yasa a kammala taron lafiya kowa ya koma gidansa lafiya.





Ya Kuma kirayi Al umma musulmai da sukasance masu hada kansu a Koda yaushe sukuma kaucewa duk abinda zai kawowa Al umma musulmai rarrabuwar Kai sukuma kasance masu nunawa juna kauna domin Samar da hadin Kai dama zaman lafiya a tsakanin Al umma musulmai.





Shima shugaban taron wato shugaban kwamitin amintattu na kungiyar dillalain maifetur ta kasa IPMAN Alhaji AbdulKadir Mbamba wailin Adamawa yabawa yayiwa wadanda suka shirya wannan taro domim a cewarsa wannan shine karo na farko da ya taba ahugabantan taro saboda haka ya gode da wannan dama da aka bashi, Kuma da yardan Allah madaukakin sarki komai zai tafi daidai ba tare da matsaloliba.







A sakonsu gawarin Ganye da Amna shelleng sun baiyana farin cikinsu dangane da shirya wannan taro domim a cewarsu wannan Yana daga cikin abinda zai kawo hadin Kai a tsakanin Al umma musulmai,



Shima a jawabinsa maimartaba Lamindo Adamawa Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa Wanda galadiman Adamawa Alhaji Mustafa Aminu ya wakilta Kiran Al umma musulmai yayi da sucigaba dayin adu a da Kuma hada Kai domin Neman taimakon Allah Madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubale dake ciwa kasan nan tuwo a kwarya.




Da yake nashi jawabi gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri Wanda shugaban ma aikatan jahar Adamawa Isa Ardo ya wakilta ya jaddada aniyarsa gwamnati da bada hadin Kai da goyon baya domin ganin an samu nasaran wajen gudanar da aiyukan cigaban jahar dama kasa baki Daya.




A jawabinsa na godiya sakataren kungiyar Jama atu Nasaril Islam a jahar Adamawa Umar Bappark Kem ya godewa daukacin sarakuna dama manyan baki wadanda suka fito daga ciki da wajen jahar Adamawa bisa halartan wannan taro da kungiyar ta ahirya ma kasa baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.