Gwamnatin jahar Taraba ta kaddamar da kungiyar ACReSAL a jahar.





Daga Sani Yarima Jalingo.

 A ranan labara da ta gabata ne gwamnan jahar Taraba Agbu Kefas ya kaddamar da kungiyar ACReSAL domin gudanar da aiyukan daban daban a jahar ta Taraba.




An gudanar da bikin kaddamar da kungiyar ne a ma aikatar muhalli da sauyin dumaman yanayi a jahar dake Jalingo fadar gwamnatin jahar.





Kungiyar Mai samun taimako daga Babban Bankin duniya domin ganin an samu cigaban inganta muhalli da Samar da ingancaccen ruwansha a yankin Arewacin Najeriya.




An kafa kungiyar ta ACReSAL ne da zumar magance kalubale danan daban da suka hada da sauyin yanayi da dai sauransu.





Kungiyar ta ACReSAL dai zata gudanr da aiyukanta ne a jihohi 19 dake Arewacin Najeriya hada da birnin tarayya Abuja. Tare da hadin Kai ma aikatun ruwa Dana harkokin noma da dai sauransu.




A jawabinsa gwamna Kefas ya baiyana gamsuwarsa da irin aiyukan cigaban kungiyar ta ACReSAL keyi don haka nema ya tabbatarwa jama a cewa a shirye gwamnatinsa take domin baiwa kungiyar goyon baya wajen gudanar da aiyukan cigaba.





Harwayau gwamna Kefas ya kaddamar da ofishin kungiyar ya ACReSAL na jahar Wanda hakan zai baiwa kungiyar damar gudanar da aiyukanta yadda ya kamata a fadin jahar.





Kwamishiniyar muhalli da sauyin yanayi a jahar Aishat Barde itace zata jagoranci aiyukan kungiyar a jahar ta Taraba a wani mataki na magance dukkanin kalubale daban daban a fadin jaha.





Kwamishiniyar ta baiyana godiyarta dangane da aiyukan kungiyar musammanma kammala aiyukan rijiyar burtsatse masu aiki da hasken rana 11 wadanda akayi a kananan hukumomi tare da suka hada da Gashaka, yero, Lau, Ardo kola, Bali, Donga, Jalingo, Kurmi, da Kuma Wukari,




Ta Kuma yabawa gwamna Kefas bisa kokarinsa na baiwa kungiyar ta ACReSAL  goyon baya wajen karasa aiyukan gudanar da wasu aiyuka a fadar gwamnatin jahar da dai sauransu.




Ta Kuma yabawa kungiyar ta ACReSAL bisa kokarinta na gudanar da aiyukan cigaban jahar da dai sauransu.





Shima a jawabinsa ko odinatan kungiyar ta ACReSAL a jahar Taraba Samaila Dumuti ya bayana cewa aiyukan kungiyar zaitaimaka wajen rage radadin wahalar rayuwa da ake ciki.




Bikin kaddamar wa ya samu halartan shugaban ma aikatan gwamna me Jeji Williams, shugaban kwamitin kan muhalli, darectoci da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE