Kungiyar kwadigo a jahar Adamawa tabi sahun takwaririnta na jihohi wajen gudanar da zanga zanga lumana.
Daga Ibrahim Abubakar Yola.
Hadakar kungiyar kwadigo a Najeriya shiyar jahar Adamawa NLC tabi sahun takwaririnta na jihohi wajen yin zanga zangar lumana na kasa baki Daya domin janyo hankalin gwamnati da tayi la akari da halin kunci da Al ummar Najeriya suka tsanci kansu a ciki.
Shugaban kungiyar a jahar Adamawa kwamuret Emmanuel Fashe ya kirayi gwamnati tarayya da tayi dukkanin maiyiwa domin ceto yan Najeriya domin yan Najeriya suna ciki wahala da Kuma tsadar rayuwa.
Emmanuel Fashe yace sun gudanar da wannan zanga zangan lumanane saboda nunawa gwamnati halin matsalar rayuwa da yan Najeriya suke ciki sakamokon hawhawar farashin kayaki a fadin Najeriya.
Fashe ya ya zama wajibi su tunatar da gwamnatin tarayya irin yanayi da ake ciki na matsatsin raguwa a fadin Najeriya saboda haka gwamnati ta farka daga barcin da takeyi ta gaggauta daukan matakin magance matsalar baki Daya.
Da yake karban wasikar bukatun hadakar kungiyar kwadigo a madadin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri shugaban ma aikatan gidan gwamnati dake nan Yola Dr Edga Amos ya tabbatarwa ma aikatan cewa gwamnatin zatayi dukkanin abinda suka dace domin ganin an rage kaifin matsanancin hali da ake ciki a jahar Adamawa.
Dr Edga ya Kuma baiyana farin cikinsa da godiyarsa dangane da yadda kungiyar kwadigo ta gudanar da wannan zanga zanga da akayishi cikin lumana ba tare da matsalaba.
Yace zai mika sakon nasu ga gwamna domin ganin sakon ta Kai ga shugaban kasa domin dubawa da Kuma daukan matakin da ya dace Akai.
Comments
Post a Comment