An Bude gasar Karatun Al Qur ani Mai girma maitake Aisha Karo na farko a jahar Adamawa.





 A Karon farko an Bude gasar karatun Al Qur ani Maigirma Mai taken Aisha Gaji Wanda Alhaji Muhammed Gwani ya assasa a jahar Adamawa.


An dai Bude gasar karantunne a makarantar Islaniyar Bornoma dake NEPA a cikin garin Jimeta a karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa.




Dake jawabi a wurin Bude gasar Modibbo Safiyanu Iya Runde Babban limamin Masallacin Jumma a na tsohon kasuwa Kuma wakilin malamai yaja hankalin Al umma musulmai wajen yiwa Al Qur ani hidima da Kuma taimakawa wajen bunkasa karatun Al Qur ani Mai girma domin samun cigaban addinin musulunci.



Modibbo Safiyanu ya Kuma kirayi Al umma musulmai musammanma mawadata da suyi koyi da Alhaji Muhammed Gwani wajen shirya irin wadannan gasa Wanda acewarsa hakan zaitaimaka wajen cigaban karatun Al Qur ani Mai girma a tsakanin Al umma.




Shima a jawabinsa Alhaji Usman Ahmed Dada Kaigaman Jimeta ya godewa daukacin wadanda suka halarci taron Bude gasar tare da Yi musu fatan Allah ya maida kowa gijensu lafiya.



Ya Kuma shawarci Al ummah musulmai da sukasance masu karanta Al Qur ani Mai girma saboda Yana da mutukan muhimmanci da Kuma lada maiyawan gaske da ake samu musammanma a cikin watan Azumin Ramadan.




Malam Hayatu Modibbo iya Runde Wanda shinema shugaban Alkalain gasar ya kirayi dalube da zasu shiga gasar da sukasance masu baiwa Alkalain hadin Kai da goyon baya domin ganin an cimma nasaran wannan gasar cikin lumana.



Ya Kuma jinjinawa Wanda ya assasa wannan gasa tare duk Wanda ya bada goyon baya wajen shirya wannan gasa tare da yin fatan Allah yasa a kammala lafiya.



Da yake zantawa da manema labarai jinkadan bayan an Bude gasar Alhaji Muhammed Gwani wandama shine ya assasa gasar ta tunawa Hajiya Aisha Gaji yace ya assasa wannan gasar ne domin irin Sha awa da yake dashi waken karatun Al Qur ani Mai girma. Wanda Kuma burinsa shine fadada karatun Al Qur ani Maigirma a jahar Adamawa, da kasa harma da duniya baki Daya.



Don haka yake kira ga matasa irinsa da Suma su taahi tsaye wajen shirya irin wannan gasa Wanda a cewarsa ya dauki tsawon lakaci Yana tunanin Bude irin wannan gasa Wanda Kuma sai a wannan lokaci ya samu damar budewa.


Alhaji Muhammed Gwani yace da yardan Allah madaukakin sarki zaiyi iya kokarinsa domin ganin an bunkasa wannan gasar zuwa fadin duniya baki Daya.



Dalube da damane dai suka shiga gasar Kuma rukunin Daya ne za a gabatar wato rukunin izu sittin ne zasu gudanar da gasar da ake saran zai dauki kwanaki goma anayi.


Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE