An bukaci da Al umma musulmai sukara himma wajen Neman ilimim Al qur ani Maigirma.
A yayinda ake cigaba da Azumin watan Ramadan an bukaci Al ummah musulmai da su Kara himma wajen karatun Al Qur ani Mai girma domin samun falalan Allah madaukakin sarki a Koda yaushe.
Shugaban karamar hukumar yola ta arewa Alhaji Nasiru Hammanjoda ne ya baiyana haka a lokacin da yake jawabi a wurin rufe gasar Karatun Al Qur ani Mai taken Aisha Gaji Wanda aka gudanar a makarantar Islamiyar Bornoma dake cikin garin Jimeta dake cikin karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Alhaji Nasiru Hamman joda yace ya kamata Al ummah musulmai su maida hankali wajen karatun Al Qur ani Mai girma da Kuma shirya irin wannan gasar Karatun Al kur ani a tsakanin dalube domin bunkasa karatun Al kur ani a tsakanin Al umma musulmai domin samun cigaba
Alhaji Nasiru kamata yayi ayi koyi da abinda wadannan bayin Allah sukayi na shirya irin wanna gasan karatun Al kur ani Wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen fadada karatun Al Qur ani a tsakanin dalube.
Shima a jawabinsa Hakimin Nasarawo Abba Alhaji Abubakar Aliyu Mustafa ya nuna godiyarsa ga wadanda suka shirya wannan gasar tare da Kiran su da su cigaba da shirya irin wannan gasar domin samun cigaban Al Qur ani.
Ya Kuma shawarci mahaddata Al kur ani da sucigaba da karatun Al kur ani da Kuma karantarwar domin samun cigaba karatun Al kur ani Maigirma a Koda yaushe.
Da yake nashi jawabi Alhaji Muhammadu Geani kaka Wanda ma shine ya jagoranci shirya wannan gasar na Aisha Gaji inda yave sun dauki matakin shirya wannan gasar ne domin fadada karatun Al kur ani Kuma yace zasu fadada wannan gasar daga matakin jahar, kasa dama duniya baki Daya.
A cewarsa dai wannan lokaci yazo musu a makare saboda haka a shekara Mai zuwa za a samu cigaba gasar yadda yakamata don haka a kimtse suke domin inganta gasar a fadin duniya baki Daya
Alhaji Muhammadu Gwani Kaka ya godewa mahalarta taron maza da mata harma da yara bisa goyon baya da hadin Kai da aka baiwa kwamitin shirya gasar a lokacin da ake gudanar da gasar.
Tunda farko a jawabinsa na maraba Mallam Ahmed Tijjani godiya yayiwa dukkanin wadanda suka bada gumawa wajen gudanar da gasar, Shima ya shawarci Daluben da kada suyi kasa a gwiwa wajen cigaba da karatun Al Qur ani Maigirma a Koda yaushe.
An dai bada kaututtuka ga wadanda sukayi nasara a gasar tare da karrama wasu daga cikin wadanda suka shirya gasar ciki harda Muhammed Gwani Kaka.
Mallam Adam Zubairu ne dai yazo na Daya. Ya baiyana jindadinsa da godiyarsa ga malamainsa dama iyayensa dangane da goyon baya da suka bashi, wajen yin karatun Al kur ani.
Comments
Post a Comment