An bukaci matasa da su rungumi harkan noma.

 



Domin ganin an samu cigaban tattalin Arziki dama Samar da aikinyi an shawarci yan Najeriya musamman ma matasa da su maida hankali wajen rungumar harkokin noma  domin dogaro da kai.


Mallam  Hamza Adam Andulhamid  shi ya bada wannan shawara a lokacinda yake gabatar da nasiha maitaken dogaro da Kai Wanda kwamitin wa azin matasa na kungiyar Izala maishekwata a Jos shiyae jahar Adamawa ya shirya Muhadara anan Yola.




Mallam Hamza Adam Abdulhamid yace harkokin noma  abune da yake da yake da mutukan muhimmanci don haka bai kamata ace yan Najeriya sunyi wasa da nomaba.

Malamin addinin musulunci yace Najeriya tana da kasa Mai fadi  Kuma duk abunda aka shuka zai fita don haka ba mafita illa a maida hankali wajen harkokin noma.




Ya Kuma kirayi gwamnatoci a dukkanin matakai da su tashi tsaye domin taimakawa matasa dama manoma Wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa harkokin noma a fadin Najeriya.


Mallam Salihu Dauda sakataren majalisar malamai na kungiyar Izala maishekwata a Jos shiyar jahar Adamawa ya kirayi matasa da su Kara himma wajen Neman sana ar dogaro da Kai domin inganta rayuwarsu yadda ya kamata.


Shima anashi jawabi shugaban kwamitin matasa  wa azin matasa Mallam Auwal Tukur yace dalilinsu na shirya wannan Muhadara shine karawa matasa kwarin gwiwar rungumar sana o I dogaro da Kai.


Saboda haka nema ya kirayi mahalarta taron da suyi amfani da sukaji domin samun cigaba yadda ya kamata.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.