An fara Tafsirin Al Qur ani Mai girma a bangaren mata Dake shelkwatar Jama atul Nasril Islam a jahar Adamawa.

 



A yayinda aka shiga watan Azumi na Ramadan kungiyar yan agaji na Jama Atul Nasril Islam bangaren mata sun Bude tafsiri Al Qur ani Mai girma da aka sabayi duk shekara.


Tafsirin dai zai gudana ne a harabar shelkwatar Jama atul Nasril Islam dake cikin garin Jimeta a karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa.


Da take jawabi a lokacin Bude tafsiri Sayyida Hindu Dahiru Usman Bauchi Wanda ma itace za ta gabatar da tafsiri ta shawarci Al umma musulmai da sukasance masu sanya tsoron Allah a zukatansu dama dukkanin aiyukansu domin samun tsira ranan gobe kiyama 



Sayyida Hindu ta Kuma Ja hankalin Al umma musulmai da su dukufa wajen yin inada a wannan watan na Ramadan domin a cewarta watane da yake da dbbin Alkherai da falala masu yawa domin duk Wanda ya dage da ibada to zai rabauta.


Ta shawarci Al umma musulmai da sukaucewa duk abinda zai bata musu inadunsu sukuma kara kaimi wajen taimakawa marassa galihu dama marayu domin Suma su samu saukin rayuwa a tsakanin Jama a.


Harwayau ta kirayi Al umma musulmai da suyi amfani da wannan lokaci na watan Azumin Ramadan wajen yin adu o I domin Neman taimakon Allah Madaukakin sarki wajen kawo dukkanin kalubalen matsalar rayuwa dake addaban kasan nan.



Itama anata jawabi Hajiya Fatima Marafa shawartan matan tayi da sukasance masu hakuri da abinda mazajensu zasu kawo musu duba da yanayin da ake ciki na matsalar rayuwa lamarin da ya haddasa hawhawan farashin kayakin masurufi. Don haka akwai bukatar mata sukasance masu hakuri domin karawa mazajen kwarin gwiwa aiwatar da abinda ya rataya a kansu.



Hajiya Fatima ta Kuma kirayi malamai musammanma wadanda zasu gabatar da wa azuzzuka a fadin Najeriya da su gudanar da wa azinda zai hada kan Al umma musulmai da Kuma samar da zaman lafiya a tsakanin yan Najeriya baki Daya 


Ta Kuma kirayi mahalarta karatukan dama wa azuzzuka da suyi amfani da abinda sukaji domin cigaban addinin musulunci yadda ya kamata. Tare da Kiran yiwa kasa adu a domin wanzar da zaman lafiya a fadin Najeriya baki Daya.


Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE