Mataimakiyar gwamna ta Bude aiyukan Samar da ruwansha a karamar hukumar Fufore dake jahar Adamawa.

 



Mataimakiyar gwamnan jahar Adamawa Farfesa  Kaletapwa Farauta ta kaddamar da aiyukan Samar da ruwansha wamda akayi a wurare biyar dake cikin karamar hukumar Fufore a jahar Adamawa.




Ana saran Samar da wadaceccen ruwansha ga jama a da dama domin magance karancin ruwansha a fadin jahar Adamawa.



Kaletapwa ta kirayi Jami an tsaro tare da sarakunan gargajiya da sukasance masu sanya ido kan kayakin don kada wasu su lalata kayakin da akayi a garuruwan da suka hada da Gurin, wuro boki, Dasin Hausa, da Kuma malabu.




Dangane da Shirin Samar da ruwa tace karamar hukumar ta dauki tsawon lokaci tana bukatar da a samarwa Al ummar ingancaccen ruwansha.




Saboda da haka nema ta kirayi wadanda suka amfana da aikin da su maida hankali sosai tare da tabbatar da cewa sun kula dashi yadda ya kamata.




A jawabinsa kwamishinan Al barkatun ruwa a jahar Adamawa Mr Audu Ayuba Tanko yace an samu nasaran gudanar da wadannan aiyuka ne biyo bayan yadda gwamnatin maici ta kudiri aniyar inganta rayuwar Al ummarta.



Kwamishinan ya baiyana cewa wurare biyar ne suka amfana da aikin ruwansha a karamar hukumar ta Fufore Wanda gwamnatin jahar tayi.



Tunda farko a jawabinsa Usman Hamman Tukur Daware shugaban karamar hukumar Fufore ya yaba tare da godewa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa wannan taimaka da yayiwa karamar hukumar acewarsa aiyukan Samar da ruwansha zaitaimaka wajen Samar da wadaceccen ruwansha dama rage wahalar da ake samu a bangaren ruwansha.




Yace aiyukan ruwan Yana daga cikin aiyukan da suke bukata gwamna yayi saboda haka nema shugaban karamar hukumar ya nemi da a kawo musu transformer domin Samar da wadaceccen wutan lanfarki.




Hakimin Ribadau na riko Aliyu Ahmed tare da masu ruwa da tsaki a sakonso na godiya sukace wannan taimako da gwamnatin fresh air tayi abun a yabane Kuma abun godiyane, saboda haka suna yabawa gwamnatin bisa wannan taimako da tayi musu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE