Mataimakiyar gwamnan jahar Adamawa tanemi hadin Kai a tsakanin Al umma.

 



Mataimakiyar gwamnan jahar Adamawa Farfesa Kaletapwa Farauta ta bukaci hadin Kai a tsakanin Al ummar jahar.


Mataimakiyar gwamna ta baiyana haka ne a lokacin da ta marabci kungiyar bangaren mata na kiristoci a Najeriya wato CAN a ziyara da suka kaimata a ofishinta dake nan Yola.


Da take jawabi Farfesa Kaletapwa Farauta ta gargadi da su kaucewa amfani da siyasa wajen kawo abinda zai haifar da matsala a tsakanin Al umma, ya kamata su maida hankali wajen yin dukkanin abinda zai kawo zaman lafiya.


Tace a matsayinsu na iyaye ya kamata a Koda yaushe sukasance masu maida hankali wajen tarbiya domin kawo karshen kalubalen da ake fuskanta.


Mataimakiyar gwamnan ta kirayi mata da suyi aiki kafada da kafada domin samun taimakon Allah Madaukakin sarki.ta Kuma shawarcesu da sucigaba dayin adu o I domin kawo ga karshen kalubalen tsaro a fadin jahar baki Daya.


A jawabinta shugabar kungiyar ta WOWICAN Princess Edna Azura  wand Kuma itace kwamitin shirya taro na shekara ta 2024 tace sun kawo ziyaran ne saboda taya mataimakiyar gwamna murnan domin samun nasara da gwamnatin tayi a kotun koli.


Azura tayi amfani da ziyaran wajen sanar da mataimakiyar gwamnan dangane da taro da za ayi a jahar daga ran 11-14-4-2024.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE