Mutane shida sun shiga komar Yan sanda a jahar Adamawa.




 Kawo yanzu rundunan yan sanda jahar Adamawa tana tsare da mutane shida da ake zargi  da satar Keken NAPEP.


Rundunan ta rundunan SCID Yola suka nasaran kama mutane biyo bayan rahoton da suka samu na satn Keken NAPEP.



Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.


 Sanarwan tace da zaran an kammala bincike za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin su fuskanci shariya.


Kwamishinan Yan sanda jahar Adamawa Dankombo Morris yabawa Jami an Yan sandan bisa wannan jajircewa da sukayi wajen kama mutanen.


Ya Kuma kirayi Al umma da sukasance masu taimakawa rundunan da wasu bayanai da zai taimaka wajen dakile aikata laifuka.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE