Rundunan Yan jahar Adamawa ta maido da zaman lafiya a kauyuka da suke kananan hukumomin Numan da Demsa.
Biyo bayan Kai ruwa rana da aka samu a tsakanin Al ummar Selfi da Pkasham wadanda ke cikin kananan hukumomin Numan da Demsa a jahar Adamawa lamaeinda yayi sanadiyar mutuwar mutane uku
Tunun dau kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankombo Morris ya tura jaimi an Yan sandan domin maido da zaman lafiya da Kuma doka da oda a yankunan.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
Sanarwan tace a yanzu haka lamura sun koma daidai Kuma ana cigaba da bincike domin kama wadanda suke da hanu a cikin rikicin.
Kwamishinan Yan sandan ya kirayi mazauna yankin da su rugumi zaman lafiya su kaucewa duk abinda zai haifar da matsala a tsakaninsu.saboda haka sugudanar da aiyukansu batare da fargaba ba su Kuma Kai rahoton duk
Wanda ba su amince da lamarinsa zuwa ga ofishin Yan sanda mafi kusa.ko Kuma Akira wadananan lambar waya.08089671313.08034037570.
Kwamishinan yan sandan ya tabbatarwa gwamnati da ma Al mar jahar Adamawa cewa rundunan zata hukunta duk Wanda aka kama da aikata irin wadannan lafika domin rundunan bazata nade hanunta tana kallo ana tada hankaliba.
Comments
Post a Comment