Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta gargadi jama a da su nisanta kansu daga karya doka.
Biyo bayan datakita zirga zirgan mashuna Wanda gwamnatin jahar Adamawa tayi a wasu wurare kamar su rukunin gidaje ta tarayya, da Ngurore, Mbaba, waru jaabbe da yolde Pate dama gadin Girei Yola ta arewa da Kuma Yola ta kudu.
Saboda haka rundunan yan sandan jahar Adamawa ta lura akwai wadanda sukegi dokan Karan tsaye don haka duk matuka mashuna dake zaune a inda dokan ta shafa to suyiwa kansu kiyamun laili da su nisanta kansu daga yin buris da dokan.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa dayarabawa manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Sanarwan ta Kuma shawarci Al umma da sunista kansu da yiwa doka karantsaye tare da tabbatarwa Al umma cewa hukumomin tsaro a kimtse suke su kare rayuka dama dukiyoyin jama a.
Kwamishinan Yan sanda jahar Adamawa Dankombo Morris ya umurci dukkanin Jami an Yan sanda da suke yankunan da dokan ya shafa da su tabbatar da cewa anbi doka da oda .
Rundunan da aka kafa domin ganin anbi wannan doka sun hada da dukkanin hukumomin tsaro wadanda zasu sanya ido a dukkanin wuraren da aka sanya sokan takaita zirga zirgan mashuna.
Comments
Post a Comment