Rundunan yan sandan jahar Adamawa tana tsare da mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane.

 



Rundunan yan sandan jahar Adamawa tare da hadin gwiwar mafarauta sunyi nasaran kama mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da mutane domin Neman kudin fansa, mutanen biyu dai Wanda rundunan ta aiyanasu dacewa ana nemanau ruwa a jallo.


Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.


Sanarwan tace an aka wadanda ake zargin ne biyo bayan samun bayanain airri  mutane biyu ana zarginsu da yin garkuwa da Saddam Ahmadu mazaunin Balel a cikin karamar hukumar Maiha, a jahar Adamawa sai Buba Adamu dake karamar hukumar Shani a jahar Borno harma sun karbi kudin fansa nera Milyon hudu da dubu Dari bakwai, 4,700,000 daga yan uwaran mutanen da akayi garkuwa da su 


Wadanda aka kamandai sun hada da Ahmed Muhammed Dan shekaru 37 da haifuwa mazaunin karamar hukumar Song a jahar Adamawa da Muhammed Haruna mazaunin anguwar Jambutu cikin karamar hukumar yola ta arewa Kuma anyi nasaran kamasune a maboyarsu.


Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa DanKombo Morris ya baiyana farin cikinsa tare da yabawa kwamandan Crack da mafarauta dama Al ummar dake tai makawa Yan sanda bisa na mijin kokari da sukeyi wajen. Kama wadanda ake zargi da aikata laifuka.


Kwamishinan ya tabbatar da cewa za a gudanar da binke yadda ya kamata domin turasu kotu domin su fuskanci shariya.


An dai gano makamai a wurin wadanda ake zargi da suka da bindiga Kiran AK 47 guda Daya da alnarushe 25.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE