Rundunan Yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran kama mutane uku da take nema ruwa a jallo

 



A kokarinta da yaki da taaddanci rundunan yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran kama mutane uku cikin jerin wadanda suke nema ruwa a jallo.



Rundunan yan sandan ta runduna ta musamman dake yaki da Yan shila ta kama mutanen ne wadanda suka addabi mutane dake Sangere dake kan titin Numan, da wuro jabbe dake cikin karamar hukumar yola ta kudu a jahar Adamawa.




Kuma an kamasu da makamai masu hatsari, irinsu wukake adduna da dai sauransu.



Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.




Biyo bayan kamasun dai tunin suka amsa laifunsu inda suka cema su sukayiwa wata daliba da take karatu a Jami ar Modibbo Adama dake nan Yola Mai Suna Lidia James kwacen waya.




Wadanda ake zargin dai sun hada da Jamilu Sanusi Dan shekaru 19 da  Yusuf Sardauna maishekaru 21 da Kuma Ma aju Abdullahi Dan shekaru 20 Wanda a yanzu haka ana cigaba da bincike kuma da zaran an kammala bincike za agurfanar da su gaban kotu domin su fuskanci shariya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE