Rundunan yan sandan Najeriya ta lashi takwabin kama duk Wanda yake da hanu a kisan Jami anta shida a jahar Delta.

 



Rundunan yan sandan Najeriya tace yanzu haka ta tsumduma cikin gudanar da bincike domin gano wadanda suke da hanu a kisan Jami an yan sanda a wani hatsaniya da ya faru a Ughelli dake jahar Delta.





Lamarin da yayi sanadiyar mutuwar Jami an Yan sanda shida inda harziwa yanzu a Kai ga gano Yan sanda shida ba.




Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da maimagan da yawun rundunan  ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a Abuja.




Biyo bayan kwararar bin cike da aka gudanar yanzu haka ana tsare da mutane takwas da ake zargi da hanu a cikin harin kwanyan bauna da akayiwa Jami an Yan sandan, tun da farko dai an kama mutane biyar, kana daga bisani an kama mutane uku a wurare daban daban. Biyo bayan hadin Kai da aka baiwa rundunan ne ya bada samun nasaran kama wadanda ake zargin Wanda jimlansu yaka takwas.





Wadanda aka kama suna tsare a hanun Yan sanda Kuma suna taimakawa wajen gudanar da bincike . Kuma runduna Yan sandan a shirye take ta kama duk wadanda suke da hanu a cikin lamarin Kuma da zaran ta kammala bincike za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.



Rundunan ta baiyana bakin cikinta dangane da aukuwar lamarin saboda an kashesune suna bakin aiki domin kare rayuka dama dukiyoyin Al umma tare da Yi musu adu a.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE