Shugaban gidauniyar fistula a Nakeeiya yasha alwashin ceto mata daga cutar yoyon fitsari.

 



Daga Ibrahim Abubakar Yola 


An baiyana cewa mata suna taka muhimmiyar rawa wajen aiyukan cigaban Al umma.


Shugaban gidauniyar Fistula a Najeriya Dr Musa Isa ne ya baiyana haka a wata sanarwa daga Jami in watsa labarainsa Ibrahim Abubakar ya fitar dangane da ranan mata ta duniya.


Dr Musa Isa yace sanya mata cikin aiyukan bunkasa aiyukan raya kasa zasu taimaka gaya wajen cigaban kasa baki Daya.


Dr Musa yace ya kudiri aniyar dukkanin maiyiwa domin inganta rayuwa mata musammanma wadanda ke fama da cutar yoyon fitsari da Kuma wadanda suka warke daga cutar.


Shugaban gidauniyar ya Kuma kirayi matan sukasance jakadun Gidauniyar wajen wayarwa mata Kai dangane da matsalar cutar ta yoyon fitsari.


Ya Kuma taya matan murnan bikin ranan matan ta duniya Kuma sukasance masu Neman sana o I daogaro da Kai domin samun damar inganta rayuwarsu yadda ya kamata.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.