Yan Sanda a jahar Adamawa sun Sha Alwashin inganta tsaro a lokacin bikin Easter.
A yayinda ake kokarin gudanar da bikin Easter na wannan shekara ta 2024 kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankombo Morris ya tabbatarwa gwamnatin jahar Adamawa dama Al ummar jahar Adamawa cewa rundunan a shirye take ta kare raguka Dana dukiyoyin Al umma a lokaci dama bayan bikin na Easter.
Kakakin rundunan yan sanda a jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
Sanarwan tace yana daga cikin aniyar Babban sifeton Yan sandan Najeriya na inganta aiyukan Yan sanda domin su samu damar kare rayuka dama dukiyoyin jama a saboda haka rundunan ta lashi takwabin inganta tsaro a fadin jahar.
Kwamishinan ya Kuma umurci dukkanin Jami an ofishishoahin Yan sanda dake fadin jahar da su tabbatar an samu ingancin tsaro a Yan kunansu tare Kuma da sanya ido a wuraren ibadu a lokacin bikin na Easter.
Rundunan ta Kuma baiyana cewa yana da muhimmanci Jami an Yan sandan su gudanar da aiyukansu bisa tsarin doka domin samun cigaban aiyukansu yadda ya kamata.
Kwamishinan ya bukaci da gwamnatin jahar dama Al ummar jahar musammanma mabiya addinin kirista da su taimakawa rundunan da wasu bayanai da zai taimaka domin ganin an gudanar da bikin Easter cikin tsanaki ba tare da matsalaba.
Comments
Post a Comment