Yan Sanda a jahar Adamawa sun takawa Yan shila birki.
Daga Ibrahim Abubakar Yola.
A kokarin dakile aiyukan Yan shila ofishin Yan sanda dake Jimeta wato Jimeta Division dake cikin karamar hukumar yola ta arewa a jahar Adamawa ta Yi nasaran kama mutane goma sha biyar Yan shila a dai dai lokacinda suke yiwa mutane fashi da makami a runde.
Rundunan tare da hadin gwiwan Yan banga sun kama mutane 15 cikin gungun mutane dake aikata ba dai daiba.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
An dai kama mutanen ne tare da makamai masu hatsarin haske. Da suka hada da wukake, adduna da dai sauransu. Tare da wayoyin hanu biyu.
Sanarwan tace da zaran an kammala bincike za a gurfanar da su gaban kotu domin su fuskanci shariya.
Comments
Post a Comment