Yan Sanda a jahar Adamawa suna tsare da wani da ake zargi da yiwa yarsa fyade
A yanzu haka rundunan yan sanda jahar Adamawa tana tsare da wani mutum Mai shekaru 42 da haifuwa bisa zarginsa da yiwa yarsa yarsa yar shekaru 9 da haifuwa fyade.
Lamarin ya farune a Kabak dake karamar hukumar Mubi ta kudu dake jahar Adamawa.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
Sanarwan ta baiyana cewa an samu nasaran kama Auwal Shuaibu Wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da matarsa Asma u Isa ta kawo ofishin Yan sanda dake Mubi.
Biyo bayan bincike da aka gudanar Wanda ake zargin ya amsa laifunsa harma ya dora halakin aukiwar lamarin dashan giya dama kwayoyi da yasha ne yasashi aikata haka.
Kawo yanzu dai kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankombo Morris ya bada umurnin gudanar da bincike kuma da zaran an kammala bincike za a gurfanar dashi a gaban kotu domin ya fuskanci shariya.
Comments
Post a Comment