Yan Sanda a jahar Adamawa suna tsare da mutane 58 bisa zarginsu da aikata laifuka daban daban a fadin jahar.

 



Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta jaddada aniyarta na ganin ta takkabe aikata laifuka a fadin jahar.



Kamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankombo Morris ne ya baiyana haka a lokacinda yake yiwa manema labarai jawabi dangane da irin nasarori da ya samu tunda ya fara aiki a matsayin kwamishinan Yan sanda a ranan 14 -2-2024.



Kwamishin Yan sandan yace tun daga ya karbi ragamar aiki Babban matsalar da aka fuskanta shine aiyukan Yan shila.



Yace a kokarin da rundunan takeyi na dakile aiyukan yan masu tada zaune tsaye rundunan tare da hadin gwiwar yan Farauta sun kutsa sansanin sambisa dake nan Yola a jahar Adamawa. Inda ma kwamishinan ya baiyana cewa sambisa ya zama matattaran Yan shila.




A samamai da rundunan ta Kai ta kama akalla mutane 40 tare da makamai masu hatsarin a wurinsu.



Kawo yanzu dai du da du rundunan tana tsare da mutane 58 wadanda ake zargi da aikata laifuka daban daban a fadin jaha da suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makamai, da dai sauransu.




Kwamishinan ya kirayi Al ummar jahar da akoda yaushe sukasance masu taimakawa hukumomin tsaro da wasu bayanai da zaitaimaka wajen magance matsalar tsaro a fadin jahar.




Kwamishinan yace a madadinsa da Jami an rundunan suna mutukan baiyana godiyarsu da jinjinarsu ga gwamna Ahmadu Umaru Fintiri dama Al ummar jahar bisa goyon baya da suke baiwa rundunan ya tabbatar da cewa ta zaran an kammala bincike kan wadanda ake zargi za a gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci shariya.



Wasu kayaki da aka gano a wurin wadanda ake zaigin sun hada da mota Kiran Tayota Prado Jeep Mai rijistan no ABJ 344 HX da Kuma matar Foma Mai nomnan rijista RUSH 79 FA da bindigogin biyu Kiran AK 47 da Kuma alnlnarushe 25 da dai saraunsu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE