An baiyana cewa hadin Kai Yana da muhimmanci i a tsakanin Al umma.
Daga Sani Yarima Jalingo.
Shugaban karamar hukumar Jalingo a jahar Taraba Dr Aminu Jauro Hassan yayi Kiran kan hadin Kai domin baiwa gwamna Agbu Kefas damar cika muradunsa na aiyukan cigaban jaha.
Shugaban yayi wannan kirane a lokacin da ake rantsar da mutane 7 masu sanya ido kan kansiloli, tare da masu bada shawaran 12 dama shugaban ma aikata Wanda aka gudanar a harabar karamar hukumar ta Jalingo.
Dr Aminu Jauro Wanda ma shine shugaban kungiyar shuwagabanin kananan hukumomi wato ALGON shiyar jahar Taraba yace Yana da muhimmanci a maida hankali wajen yin dukkanin abinda zai kawo cigaban Al umma.
Dr Jauro ya shawarci sabbin wadanda aka rantsar din da su taka nasu rawan da zai kawo cigaba a dukkanin Al umomin yankin.
Ya Kuma yabawa gwamna Agbu Kefas bisa kokarinsa na gudanar da aiyukan cigaban jahar.
Comments
Post a Comment