An bukaci hukumar lekan asirin kasar Turkiya da ta shiga tsakani domin warfare ta kaddamar dake tsakanin Iran da Israila.
A wani gagarumin mataki na diflomasiyya, daraktan hukumar leƙen asirin Amurka William Burns ya tuntuɓi Ibrahim Kalin, shugaban Hukumar Leƙen Asirin Turkiyya (MIT), inda ya roƙe shi ya sulhuta Isra'ila da Iran.
Tattaunawar da Kalin da kuma Burns suka yi a lokacin bukukuwan ƙaramar sallah ta shafi batun tsagaita wuta a Gaza, inda Isra'ila ta ƙaddamarda hare-hare tun ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.
Bayan tattaunawarsu da takwaransa na Amurka, Kalin ya gudanar da taro a Hamas, inda ya bayyana aniyar Turkiyya wajen samun masalaha ta diflomasiyya game da rikicin da ke faruwa tsakanin ɓangarorin biyu.
Rundunar soji ta musamman ta Iran mai suna Revolutionary Guard Corps ta ƙaddamar da jerin hare-hare da jirage maras matuƙa da makamai masu linzami a Isra'ila ranar Asabar da tsakar dare don yin martani game da harin da Isra'ila ta kai ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Damascus, babban birnin Syria ranar 1 ga watan Afrilu.
Harin ya yi sanain mutuwar zaratan sojojin Iran guda bakwai, ciki har da masu muƙamin janar guda biyu, lamarin da ya jawo zazzafan martani daga jami'an gwamnatin Iran inda suka sha alwashin ɗaukar fansa.
Jirage marasa matuƙa da makamai masu linzamin da Iran ta harba ranar Asabar shi ne karo na farko da ta cilla makamai kai-tsaye daga cikin ƙasarta zuwa cikin Isra'ila.
Bayanai su ce mahukunta a Tehran sun kwashe awanni suna harba jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami fiye da 300, ko da yake Isra'ila ta kakkaɓo da dama daga cikinsu.
Ƙawayen Isra'ila irin su Amurka da Birtaniya da Faransa sun taimaka wurin kakkaɓo makaman.
Ministan Harkokin Wajen Iran Hossein Amirabdollahian ya ce sun kammala yin ramuwar gayya, ko da yake ya yi gargaɗi cewa ƙasarsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba idan Isra'ila ta sake taƙalar ta da faɗa.
Comments
Post a Comment