An bukaci masu son shiga aikin Yan sanda da su baiyana asibintin domin gwajin lafiyarsu.
A yayinda ake cigaba da aikin deban Jami an yan sanda rundunan yan sanda na shiya ta uku ta sanar da cewa za a fara tattance lafiya dama gwajin zahiri wanda za a fara daga ran 16- 30-4-2024.
Mai hulda da jama a na shiya ta uku SP Yusuf Adamu Muhammed ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
Kuma ana bukatan masu son shiga aikin Dan sanda daga jihohi biyu wato Taraba da Adamawa wadanda ke karkashin shiya ta uku da su baiyana da fararen Riga da gajeren wando a asibintin Yan sanda dake Yola. Bugu da Kari an bukacesu da suzo da Katin shaidar Dan kasa. Da Kuma takardan da ke dauke da bayanin lafiya harma da wasu takardu da suke da halaka da haka, ko kuma su ziyarci shafin yanan gizo https://apply.policerecruitment.gov.ng
Saboda haka mataimakin Babban sifeton yan sandan Nijeeiya dake kula da shiya ta 3 AIG Afolabi Babatola Adeniyi ya taya wadanda sukayi nasaran murna Kuma gwajin kautane.
Comments
Post a Comment