An jajintawa yan kasuwar Yola biyo bayan gobara da akayi.

 



Gidauniyar Attarahum dake kananan hukumomi Yola ta kudu da Yola ta arewa sun jajintawa Yan kasuwa Yola bisa iftala I gobara da ta auku a kasuwar Yola ta kudu a kwananan.

Gidauniyar ta baiyana haka ne ta bakin shuwagabanin Gidauniyar ta Attarahum da suka hada da Malam Abubakar Sadiq na yola ta arewa da Malam Mahmud Dikko na Yola ta kudu inda sukayi adu ar Allah madaukakin sarki ya kare ma gaba.


Shuwagabanin sun Kuma shawarci Yan kasuwa da sukasance masu gudanar da kaauwancinsu bisa tsaron Allah da Kuma bin dokokin Allah dangane da harkokin kasuwanci. Wanda hakan zaitaimaka wajen kare aukuwar lamarin.


Sun Kuma kirayi gwamnatin dama kungiyoyi da su gaggauta taimakawa wadanda gobaran ta shafa domin rage musu radadin wahalar da suke ciki domin ganin basu tagaiyaraba 


Tare da shawartan Yan kasuwa da sucigaba da yin adu o.i a Koda yaushe domin samun cigaban aiyukansu da Kuma samun kariya a kasuwancinsu.

Gidauniyar ta Attarahum tana Mai adu ar Allah madaukakin sarki ya kare ya Kuma mayarsu musu da Alheri, ya Kuma basu daman jimre hakuri rashin da sukayi na kayakinsu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE