An rantsar da sabbin shuwagabanin kananan hukumomi Sha Daya a jahar Gombe..
Gwamnan jahar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya kirayi sabbin shuwagabanin kananan hukumomi da sukasance masu gudanar da aiyukansu bisa tsoron Allah domin samun cigaba.
Gwamnan Inuwa Yahaya yayi wannan kirane a lokacin yake jawabi a wurin bikin rantsar da zababbun shuwagabanin kananan hukumomi Sha Daya dake fadin jahar biyo bayan kammala zaben kananan hukumomi da akayi a ranan asabar da ta gabata.
Gwamna Inuwa Yahaya ya kirayi sabbin shuwagabanin da su maida hankali wajen gudanar da aiyukan cigaban yankunansu.
Gwamnan ya Kuma taya sabbin shuwagabanin murnan lashe zabe da sukayi tare da shawartansu da su kaucewa banbance banbancen siyasa ta sukasance masu yin aiki tare domin cigaban Al ummah.
Da yake magana a madadin sabbin shuwagabanin shugabar karamar hukumar Shongom Fatima Binta Bello ta godewa gwamna bisa wannan dama da ya basu Wanda zasuyiwa Al Umarsu aiki tace zasuyi dukkanin maiyiwa domin gudanar da shugabanci na gari domin samun cigaban yankunansu.
Comments
Post a Comment