An sako dalube biyu wadanda akayi garkuwa dasu daga Jami ar tarayya a jahar Taraba.
Daga Sani Yarima Jalingo.
Rahatanin daga jahar Taraba na cewa yanzu haka a sako daluben Jami ar tarayya dake Wukari biyu wadanda akayi garkuwa dasu na tsawon kwanaki.
Shugabar sashin yada labarain Jami ar mis Ashu Agbu ce ta sanar da haka a wata sanarwa da ta fitar, sai dai sanarwa bai baiyana ko anbiya kudin fansa ko ba abiyaba kawo yanzu daluben suna cikin koshin lafiya.
In za a iya tunawa dai a ranan kahadi da ta gabata mis Agbu ta shaidawa manema labarai ce masu garkuwa da mutanen sun nemi kudin fansa na Milyon hamsin.
Comments
Post a Comment