Ana daf da gudanar da zabe na kananan hukumomi a jahar Gombe.

 



A yayinda aka fuskanci zabukan kananan hukumomin a jahar Gombe, shugaban jam iyar A P C na kasa Abdullahi Umar Ganduje ya mikawa Yan takaran shuwagabanin kananan hukumomi tura domin tunkaran zaben kananan hukumomin da za ayi ranan 27-4-2024.


Da yake mika tutoci wa Yan takaran goma sha Daya a dandalin wasa dake Pantami a jahar Gombe shugaban jam iyar A P C na kasa ya yabawa Al ummar jahar ta Gombe bisa karamci da nuna yakamata da sukayi Wanda hakan ya nuna cewa Gombe jahar APC ce. Tare da Kiran su da sucigaba da baiwa gwamnatin gwamna Muhammed Inuwa Yahaya goyon baya domin ganin ya samu nasaran gudanar da aiyuka dama tsare tsaren  da zai Kai ga jahar cigaba.




Ya Kuma kirayi masu kada kuri a da su fito ranan zabe domin zabar Yan takaran jam iyar ta APC tare da tabbatar musu da cewa gwamnatin maici a yanzu karkashin jagoranci Bola Tinubu ta dauki dukkanin matakai da suka dace domin samun cigaban kasa baki Daya.



Abdullahi Ganduje Wanda tsohon gwamnan Kano ne ya Bude wasu aiyukan gyaran hanyoyi da akayi a cikin fadar gwamnatin ya jahar Gombe, harma ya karbi wasu da suka sauya shekara daga jam iyoyi karamarsu  PDP, ANPP, SDP, da dai sauransu zuwa jam iyar APC.



Da yake jawabi a wurin bikin gwamnan jahar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya godewa  Abdullahi Ganduje dangane da zuwansa jahar Wanda wannan ya nuna cewa a kwai kakkawar halaka a tsakanin jam iyar APC ta kasa da jahar ta Gombe.



Gwamnan ya kirayi daukacin masu kada kuria dake fadin jahar da sufito kwanau da kwarkwatarsu domin zaben Yan takaran jam iyar ta APC a matsayin shuwagabanin kananan hukumomin dake fadin jahar dama kansiloli domin wannan gwamnati maici ta kimtsa tsaf domin gudanar da aiyukan cigaban jahar.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE