Anja hankali masu sayarda hatsi su daina tauye mudu.
Daga Sani Yarima Jalingo.
Wani malamin addinin musulunci a jahar Taraba ya gargadi masu Saida hatsi da su kaucewa tauye mudu domin biyan bukatansu, domin a cewarsa Allah zai hukunta duk Mai tauye mudu a rana tashin Al kiyama.
A sakonsa na Sallah Khadi Abubakar ya kirayi musulmai duniya da suyi amfani da wa azozi da aka gudanar a cikin watan Ramadan da Kuma sanya tsaron Allah a zukata.
Ya kirayi musulmai da sukasance masu gudanar da kyakkawar aiyuka domin Neman yardan Allah madaukakin sarki da Kuma yafiya. Tare da kaucewa dukkanin abinda zai Sa su aikata Haram da Kuma yiwa shuwagabanin adu a a Koda yaushe.
Khadi ya Kuma danganta matsalar rayuwa da ake ciki da aiyukan shedan don haka ya kirayi yan Najeriya da su koma ga Allah madaukakin sarki domin Neman taimakonsa da tausayawarsa.
Harwayau ya sahawarci yan Najeriya da sukasance masu taimakawa marassa galihu domin rage radadin wahalar da ake ciki a halin yanzu.
Comments
Post a Comment