Galadima Muri ya taya musulmai murna tare da Kira da a hada Kai.
Daga Sani Yarima Jalingo.
Alhaji (Dr) Lamido Abba Tukur Kuma Galadiman masarautar Muri a jahar Taraba ya taya Al ummar musulmai duniya murna kammala Azumin watan Ramadan da Kuma yadda aka gudanar da bikin karamar Sallah lafiya.
Dr Tukur a sakonsa na bikin Sallah ya taya Gwamna Agbu Kefas da Sarkin Muri Alhaji Abbas Njidda Tafida dama daukacin Al ummar jahar Taraba bisa kammala Sallah lafiya.
Ya jaddada farin cikinsa dangane da yadda komai ya gudanar cikin lumana tare da Kiran Al umma musulmai da suyi amfani da abinda aka koya a lokacin wata Ramada domin cigaban Al ummah.
Ya Kuma gargadi jama a da su kaucewa duk abinda zai kawo batanci ga shuwagabanin don haka kanatayayi sukasance masu yin adu o I domin Neman taimakon Allah Madaukakin sarki wajen magance dukkanin kalubalen dake ciwa Al umma tuwo a kwarya
Harwayau Dr Tukur ya yabawa gwamnatin jahar Taraba da hukumomin tsaro bisa kokarinsu na tabbatar da ganin an inganta zaman lafiya Wanda Kuma shine aniyar gwamna Agbu Kefas domin samun cigaban jahar baki Daya.
Comments
Post a Comment