Gwamnan jahar Taraba ya taya Al ummar musulmai jahar murnan bikin karamar Sallah.
Daga Sani Yarima Jalingo.
Gwamnan jahar Taraba Agbu Kefas ya taya Al ummar musulmai jahar murnan bikin karamar Sallah Wanda ake gudanarwa a karshen watan Ramadan.
Hakan yana kunshene a cikin wata sanarwa daga mashawarci gwamnan na musamman akan harkan yada labarai da ya fitar a Jalingo.
Gwamnan bayan ya taya musulmai murna ya Kuma kirayi Al umma musulmai da su Kara kaimi wajen hadin Kai a tsakanin addinai dake fadin jahar.
Ya Kuma Kara da cewa su sadaukar da Kai wajen yin aiki da abinda aka koya a cikin watan Ramadan domin samun cigaba.
Gwamnan ya Kuma baiyana cewa kasa tana bukatar adu a da kaucewa son zuciya da Kuma gudanar da shugabanci na gari Wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen magance dukkanin kalubale dake ciwa kasar tuwo a kwarya.
Gwamna Kefas yace ya lura manyan addinin biyu dake fadin jahar suna gudanar da bubukuwarsu tare Wanda Kuma haka wani cigabane matuka musamman waje kautata halaka a tsakaninsu.
Ya tabbatarwa Al ummar jahar cewa gwamnatinsa zata cigaba da kautatawa kowa da Kuma yin aiki da kowa domin samun moriyar domokiradiya.
Harwa yau gwamnan ya kaiwa Sarkin Muri Alhaji Abbas Njidda gaisuwar a fadarsa dake Jalingo Wanda Kuma shine karo na farko a tarihi a fadin jahar.
Comments
Post a Comment