Gwamnatin jahar Adamawa ta nuna damuwarsa dangane da aikata laifuka a fadin jahar.

 



Daga Ibrahim Abubakar Yola.


Gwamnatin jahar Adamawa tayi Allah Wadai da aiyukan bata gari a tsakanin Jama a domin a cewarta wannan karya doka ne.



Mataimakiyar gwamnan jahar Adamawa Farfesa Kaletapwa Farauta ce ta baiyana haka a lokacin da ta gudanar da taron manema labarai a Yola.


Farfesa Kaletapwa Farauta aiyukan Yan shila yayi kamari don haka akwai bukatar daukan matakin da suka dace domin magance matsalar.

A cewarta gwamnatin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri zatayi kasa a gwiwaba wajen tunkaran lamarin domin magance matsalar baki Daya.


Ta ce aiyukan bata gari da suka hada da kwace waya, shiga gidaje, da sauransu Wanda gwamnati baza ta lamuntaba Kuma duk Wanda aka kama da aikata laifuka zai fuskanci hukunci.


Mataimakiyar gwamnan tama zanyano wuraren da lamarin yayi kamari da suka hada Bajabure, rukunin gidajen tarayya, Badarisa, Jambutu, Shagari, da Damilu dake cikin garin Jimeta wadannan wurare suyi kaurin suna wajen aikata laifuka.


Don haka nema gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya kaddamar da rundunan operation Farauta Wanda zatayi yaki da duk masu aikata laifuka a fadin jaha.


Saboda haka a kwai bukatan iyaye su bada ta su gudumawan domin ganin an kawo karshen matsalar baki Daya.


Farauta ta Kuma baiyana cewa akwai bukatar hada hanu wajen yaki da aikata laifuka domin kawar da bata gari a tsakanin Al umma.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE