Gwamnatin jahar Borno ta amince da Sama da nera bilyon 1.5 domin Samar wa Yan jahar gurbin karatu.

 



Daga Ibrahim Abubakar Yola.


A kokarinsa na farfado da jahar Borno bayan da rikin boko Haram ya daidaita gwamnan jahar Umarana Zulum a hukumance y kaddamar da Shirin bada gurbin karatu ga asalin yan jahar da zaici kudi har nera bilyon Daya da digo biyar wato bilyon 1.5, ga daluben dake karatun aikin jinya da Ngozoma wadanda suka fito daga kananan hukumomi 27 dake fadin jahar.



Gwamnan yace an dauka matakin haka ne domin magance matsàloli da ake samu a lokacinda mata ke haifuwa lamarin yake sanadiyar rasa rayukan matan.



Tun kafin wannan na gwamnan Zulum ya kashe Sama da nera bilyon shida bayan ya amince da bada gurbin karatu ga dalube wajen karatun digiri.



Saboda haka nema gwamnan yace nan bada dadewaba kwalejin horar da ma aikatan jinya wadanda ke Gwaza da Mongono zasu fara aiki Wanda tuninma ya amince da Samar da cibiyar fasahar da sauransu domin dalube.



Shugabar kwalejin horar da ma aikatan jinya da fasahar a jawabinta tace gwamna Zulum Yana da aniyar inganta sashin kiwon lafiya a fadin jahar.wanda Kuma hakan zaitaimaka wajen cigaban jahar baki Daya.



Shima a jawabinshi kwamishinan ilimi da fasaha da kimiya a jahar injiniya Lawan Abba yace nera bilyon shida da gwamnan ya amice Kuma aka Samar da gurbin karatu wa dalube na ciki da wajen Najeriya.



Itama anata bangaren majalisar Ma aikatan jinya ta kasa ta yabawa gwamna Zulum bisa wannan namijin kokari da yayi na bada gurbin karatu. 

A karshe dai kowane dalubi ya koma gida da nera dubu Dari.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.