Gwamnatin jahar Borno ta jaddada aniyarta na bunkasa harkokin noma a fadin jahar.
Daga Ibrahim Abubakar Yola
kamar yadda kuka sani, gwamnatin jihar Borno ta ba da fifiko wajen bunkasa harkar noma a jihar, don haka ne ake kokarin hada karfi da karfe domin bunkasa noma a jihar. Gwamna Zulum yace Don haka gwamnatin jihar ta sayo injunan noma da kayan aiki kamar taraktoci da Sinadarai da takin zamani har ma da sauransu.
Gwamna Zulum ya kuma bada tabbacin ci gaba da taimakon manoman jihar. Ya ci gaba da cewa yayi imani zai taimaka matuka wajen bunkasa noman noma, don haka gwamnati ta shirya tsaf don ganin an taimakawa manoma ta kowace fuska domin kara yawan amfanin gona.
Zulum ya bayyana haka ne a ranar Talata a Maiduguri yayin bikin kaddamar da shirin tallafa wa mata na aikin gona na Renewed Hope Initiative (RHI-WASP).
(RHI-WASP) wani shiri ne na uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, na tallafa wa mata masu gudanar da ayyukan noma da bayar da gudumawa wajen samar da wadataccen abinci na shugaba Tinubu.
Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta samu wakilcin uwargidan mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Kashim Shettima a wajen taron.
Kimanin mata manoma da nakasassu 220 ne suka ci gajiyar shirin; Daga cikin su, mata manoma 120, Daga kowace jaha achin jahohi 6 na arewa maso gabas mutum 20 sun karbi Naira 500,000. Sannan kuma nakasassu 100 daga Borno kowanne ya samu N100,000.
“A yau muna tallafa wa mata manoma ashirin (20) kowace jiha a shiyyar Arewa maso Gabas da kudi Naira dubu dari biyar kowacce, in ji Uwargidan shugaban kasar.
Ta kara da cewa, "Za a mika kudaden ga matan gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba, da Yobe wadanda suka kasance.
Comments
Post a Comment