Hakimin Nasarawo Abba yayi kira wajen Samar da hadin Kai a tsakanin Al ummah.

 



Hakimin Nasarawo Abba Kuma sarkin Sudan Adamawa Alhaji Abubakar Aliyu Mustafa ya kira dangane da hadin Kai a tsakanin Al ummar masarautar Nasarawo Abba domin Samar da cigaba da zaman lafiya a yankin.


Hakimin yayi wannan kirane a lokacinda masu jimilli da masu angwanni dama kungiyoyi  harma da masu rike da masarautun gargajiya a yankin, suka Kai masa gaisuwar Sallah a fadarsa dake Nasarawo Abba dake karamar hukumar yola ta Arewa a jahar Adamawa.


Hakimin yace hadin Kai abune da yake da muhimmanci a tsakanin Jama a don haka akwai bukatan Al umma sukasance masu hada kansu a Koda yaushe domin Samar da zaman lafiya a Mai daurewa.



Hakimin Alhaji Abubakar ya shawarci Al umma na Nasarawo Abba da su cigaba da yin adu o I domin Neman taimakon Allah Madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubale da ake fuskanta na rayuwa.

Saboda haka Hakimin ya yabawa Al ummar Masarautar Nasarawo Abba bisa kokari da suke daahi na rungumar zaman lafiya da kowa saboda haka Yana da muhimmanci sukasance masu baiwa masarautar goyon baya da hadin Kai domin ganin masarautar ta samu damar gudanar da aiyukan cigaban yankin.


Tunda farko a jawabinsa Alhaji Saidu Buba wakilin masallatai Nasarawo Abba yace sun kawo ziyaran fadar hakiminne domin gaisuwar Sallah tare da taya Hakimin murnin bikin Sallah.


Alhaji Saidu ya yabawa Hakimin bisa kokarinsa da hada kan Al umma yankin na Nasarawo Abba Wanda hakan zai taimaka wajen cigaban yankin.


Ya Kuma tabbatar da cewa Al umma yankin na Nasarawo Abba a shirye suke su marawa masarautar baya a Koda yaushe domin samun cigaban masarautar ta Nasarawo Abba.


Cikin kungiyoyi da suka kaimasa ziyara gaisuwar Sallah sun hada da Kungiyar Nasarawo Lummo Koppi Youth Association NALYA . da kungiyar Rayuwar a yau RAYASS da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE